in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Motsa jiki a karshen mako yana da amfani kamar yadda ake motsa jiki a ko wace rana
2018-02-23 14:15:27 cri

Wadanda ba sa iya motsa jiki a ko wace rana sakamakon fama da aiki, watakila ba su lura da wannan sabon sakamakon nazari ba! Idan har suna motsa jiki a karshen mako, haka zai taimaka wajen rage barazanar mutuwa da suke fuskanta sosai.

Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta ba da shawarar cewa, kamata ya yi a dauki mintoci a kalla dari 1 da 50 ana motsa jiki a hankali, ko kuma mintoci 75 ana motsa jiki da karfi. Amma a rika tattaunawa a tsawon lokacin da ake dauka a ko wace rana yayin da ake motsa jiki. Mutane da yawa suna fama da aiki kullum,wannan ya sa ba sa samun lokacin motsa jiki sai karshen mako, lamarin da ake ta shakkar amfaninsa ga lafiyar mutane.

Masu nazari daga kasar Australia sun kaddamar da rahoton nazarinsu a kwanan baya, inda suka tantance bayanan da suka shafi yadda 'yan Birtaniya kusan dubu 64 suka motsa jikinsu da yadda suka mutu daga shekarar 1994 zuwa 2012. A cikin wadannan shekaru, wasu mutane 8802 sun rasu ne sakamakon dalilai iri daban daban, alal misali wasu 2708 sun mutu ne sakamakon cututtukan zuciya da na magudanar jini, kana ciwon sankara sun halaka wasu fiye da 2500.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, muddin mutum ya motsa jiki, hakan zai taimakawa wajen kyautata lafiyarsa ko lafiyarta. Idan aka kwatanta su da wadanda ba su taba motsa jiki ba, ko dai su kan motsa jiki sau daya ko biyu a karshen mako, amma tsawon lokacin motsa jiki da suka dauka ya kai matsayin da aka wajabta na motsa jiki, barazanar mutuwa da suke fuskanta zai ragu da kashi 30 cikin dari, a ciki kuma yawan mace-mace sakamakon cututtukan zuciya da na magudanar jini ya ragu da kashi 40 cikin dari, yayin da yawan barazanar mutuwa sakamakon ciwon sankara shi ma ya ragu da kashi 18 cikin dari.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, sakamakon nazarinsu ya faranta rayukan mutane kwarai gaske. Akwai alaka a tsakanin motsa jiki sau daya ko biyu a ko wane mako da kuma raguwar yawan mace-mace. Amma duk da haka, sun kara da cewa, idan ana fatan ganin motsa jiki ya taka rawa kamar yadda ake fata, ya fi dacewa a motsa jiki kamar yadda hukumar WHO ta ba da shawara.

Masu sharhin sun kuma gabatar da ra'ayoyinsu cewa, sakamakon nazarin ya nuna mana cewa, tabbas motsa jiki ya fi rashin motsa jiki muhimmanci a fannin rage yawan mace-mace. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China