in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila cin sinadarin Bitamin B da yawa cikin dogon lokaci zai kara wa maza barazanar kamuwa da ciwon sankarar huhu
2018-03-19 06:42:35 cri

Kwanan baya, mujallar ilmin cutar sankara ta kasar Amurka ta kaddamar da wani sabon sakamakon nazari da ke cewa, shan magani mai sinadarin Bitamin B6 da na B12 da yawa na tsawon lokaci zai kara wa maza barazanar kamuwa da cutar sankarar huhu, musamman ma masu shan taba.

An dade ana daukar sinadarin Bitamin B6 da B12 a matsayin wadanda suke iya kara karfi ga mutane, taimakawa wajen sarrafa sinadaran jiki, da rage barazanar kamuwa da cutar sankara. Amma bayan da masu nazari daga jami'ar jihar Ohio ta Amurka suka dauki shekaru 10 ko fiye da haka suna bincike kan Amurkawa baligai kimanin dubu 77, sun gano cewa, idan aka dauki lokaci mai tsawo ana shan magani mai sinadarin Bitamin B6 da B12 fiye da kima, watakila sinadarin zai iya kawo illa ga lafiyar mutane.

Nazarin ya shaida mana cewa, idan maza suka sha magani mai sinadarin Bitamin B6 da yawansa ya wuce milligram 20 a ko wace rana, ko kuma suka sha magani mai sinadarin Bitamin B12 da yawansa ya wuce milligram 55 a ko wace rana, to bayan shekaru 10, barazanar da za su fukanta wajen kamuwa da cutar sankarar huhu za ta ninka sau daya. Har ila yau kuma, idan kuma suka sha taba, barazanar da za su fuskanta za ta karu sau 3 zuwa 4 gwargwadon sauran mutane.

A halin yanzu, hukumomin Amurka masu ruwa da tsaki sun bai wa maza shawara dangane da adadin sinadarin Bitamin B6 da ya kamata sha a ko wace rana, wato milligram 1.5, kana kuma, kada su wuce sinadarin Bitamin B12 da suke sha a ko wace rana, wato milligram 2.4.

Masu nazarin daga jami'ar jihar Ohio sun yi nuni da cewa, yanzu yawan sinadarin Bitamin B da ke cikin ko wane maganin sinadarin da ake sayarwa a kasuwa a halin yanzu ya wuce adadin da aka ba da shawarar a sha. Hakika dai, mutane suna iya samun isasshen sinadarin Bitamin B ta hanyar cin nama, wake, da hatsi. Don haka babu bukatar a sha magani mai sinadarin Bitamin B da yawa na shekara da shekaru. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China