in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara yawan kofi da ake sha zai taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar hanta
2018-03-05 06:23:23 cri

Wata kungiyar masana ta kasar Birtaniya ta kaddamar da rahotonta a kwanan baya, inda ta nuna cewa, shan kofi a ko wace rana yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar hanta. Kana sakamakon ya nuna cewa, kara shan kofin, ya sa barazanar kara raguwa, lamarin da ya goyi bayan sakamakon nazarin da aka samu a baya, wato shan kofi yana iya rage barazanar kamuwa da cutar sankarar hanta.

Masu nazari daga jami'ar Southampton da ta Edinburgh sun yi nazari kan alakar da ke tsakanin shan kofi da kuma cutar sankarar hanta. Masu nazarin sun tantance bayanan da aka samu a baya daga nazarce-nazarce guda 26, wadanda mutane fiye da miliyan 2 da dubu 250 suka shiga cikin nazarce-nazarcen. Wasu nazarce-nazarce da aka yi a baya a kasashen Amurka da Japan sun nuna cewa, shan kofi yana iya ragewa mutane kamuwa da cutar sankarar hanta.

Sakamakon sabon nazarin ya shaida mana cewa, shan kwaf guda 1 na kofi a ko wace rana yana iya rage barazanar kamuwa da cutar sankarar hanta da kashi 20 cikin dari. Shan kwaf guda 2 na kofi a ko wace rana kuma yana iya rage barazanar da kashi 35 cikin dari. Yayin da shan kwaf guda kogi 5 a ko wace rana kuma yana iya rage barazanar da kashi 50 cikin dari.

Masu nazarin sun yi bayani cewa, ko da yake adadin ya shaida cewa, kara shan kofi yana iya kara rage barazanar, amma idan mutum ya sha kofi fiye da kwaf guda 5 a ko wace rana, ya zuwa yanzu babu iya adadin da suka iya tabbatar da raguwar barazanar. Ban da haka kuma, shan kofi da babu sinadarin Caffeine shi ma yana iya rage barazanar, duk da cewa bai kai yadda ake zato ba.

Ya zuwa yanzu masana ba su tabbatar da tasirin da kofi yake yi kan lafiyar mutane ba. Kafin wannan kuma, cibiyar nazarin cutar sankara ta kasa da kasa dake karkashin kulawar hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO tana daukar shan abu mai matukar zafi a matsayin dalilin da watakila zai sanya a kamu da cutar sankara. Hukumar tana ganin cewa, mai yiwuwa ne shan kofi da shayi da sauran abubuwa da zafinsu ya wuce digiri 65 kullum zai sanya a kamu da cutar sankarar makogwaro.

Masu nazarin na Birtaniya sun yi nuni da cewa, sakamakon nazarinsu bai karfafawa mutane gwiwar su sha kwaf guda 5 na kofi a ko wace rana ba. Ana bukatar nazari mai zurfi domin tabbatar da illar da shan kofi da yawa za ta haifar ga lafiyar mutane, wadda ba a gano ba tukuna. Har ila yau kuma, akwai shaidu da suka nuna cewa, wasu mutane na musamman, kamar masu juna biyu, bai kamata ba su sha irin wannan abun sha fiye da kima. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China