A ra'ayina, a karshen wannan ziyara za a iya samun fahimta mai kyau ta yadda duk kan bangarori biyu zasu kara infanta har kuma a ci riba ko a rika cin moriyar juna.
Kwanan baya, jakadan Sin dake Nigeria Mista Zhou Pingjian, kwamishina mai kula da harkokin kasuwanci Mista Zhao Linxiang da dai sauran wakilan ofishin jakadancin kasar Sin sun kai ziyara a jihar Jigawa, inda sun gana da gwamnan Jigawa Badaru Abubakar, gwamnan Jigawa ya taba kai ziyara sau da dama a kasar Sin don neman hadin gwiwa tsakanin jiharsa da kasar Sin. Wakiliyarmu Amina ta yi rakiya ga jakada, kuma ta zanta da gwamna, ga rahoton da ta hada mana.