in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na saurari shirin 'Allah daya gari bamban' na musamman
2016-11-06 11:20:39 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri gare ku, da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing.

Ina farin cikin sanar da ku cewa, na samu ikon sauraron sabon shirin ku na "Allah daya gari bamban" na yau Jumu'a 4 ga wata, wanda ya kasance na musamman ne dauke da cikakkiyar hirar da aka yi da malamai Murtala Zhang da Amina Xu a gidan rediyon Aso FM da ke birnin Abuja.

Hakika na ji dadin sauraron zantawar da aka yi da sabuwar wakiliyar CRI Hausa a Abuja wato Amina Xu da kuma tsohon wakilin CRI mai barin gado Murtala Zhang Weiwei. Koda yake, a nan jihar Kano inda nake zaune ba ma iya kama tashar Aso FM. Amma bisa gudunmawar CRI Hausa na samu zarafin sauraron wannan hira da ta yi dadi sosai kuma ta nishadantar matuka.

Dangane da haka, ina mika godiyata ta musamman ga CRI Hausa bisa wannan tsaraba da suka kawo mana. Har ila yau, ina son yin amfani da wannan dama wajen yin fatan alheri ga sabuwar wakiliyar CRI Hausa malama Amina Xu da kuma shi malam Murtala Zhang dake shirye shiryen komowa birnin Beijing domin ci gaba da gudanar da aiki a sashen Hausa.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China