in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malama Amina xu ta zo taraiyar Nigeria lafiya kalau
2016-11-06 11:19:34 cri

A ranar 19 ga watan 10 shekara ta 2016, malama Amina Xu ta sauka a birnin Abuja taraiyar Nigeria inda za ta maida gurbin aikin malam Murtala zhang tsohon wakilinku a birnin Abuja taraiyar Nigeria. Jim kadan da saukarta a birnin Abuja Nigeria na samu zarafin gaisawa da ita kuma na mata lale marhabum da zuwa birnin Abuja Nigeria. Agaskiya malama Amina Xu ta kware sosai kuma tana da hazaka da kokarin aiki sosai, amma za mu dade muna jimami da kuma kewar barin aikin malam Murtala Zhang a matsayin wakilin cri Hausa a taraiyar Nigeria. Daga shekarar 2012 da malam Murtala Zhang ya fara aiki a matsayin saban wakilin sashin Hausa na cri a taraiyar Nigeria, ya yi aiki tukuru har zuwa karshen aikinsa a Nigeria a 2016. A zamanin da yake aiki a Nigeria, malam Murtala Zhang ya yi kokari sosai wajen sada zumunci da mu masu sauraro kana ya taimaka ainun wajen fadakar da al'ummar Nigeria da duniya hakikanin abun dake toyawa tsakanin taraiyar Nigeria da aminiyarta kasar Sin ta fannin kasuwanci da kuma dangantakar diplomasiyya da dai sauransu. Kazalika, malam Murtala zhang ya kware ainun wajen fadakar da masu sauraro rahotanni masu dumi-dumi daga birnin Abuja. Agaskiya mun ji dadin yin hulda da malam Murtala Zhang, da fatan watarana za mu kara yin hulda da malam Murtala zhang a matsayinsa na saban wakilin cri Hausa a karo na 2, amin. Haka nan, mu masu sauraro mun shirya tsaf domun ba wa sabuwar wakiliyarku malama Amina Xu goyan baya da hadin kai a wa'adin aikinta a taraiyar Nigeria.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China