in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawara dangane da sakonnin masu sauraro a shafin CRI Hausa na Facebook
2016-10-13 08:59:58 cri
Zuwa ga sashen Hausa na rediyon kasar Sin CRI.

Tare da fatan daukacin ma'aikatan sashen Hausa na CRI suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ina son gabatar mu ku da wata sabuwar shawara dangane da sakonnin da masu sauraro ke rubutawa a shafin ku na Facebook, wato irin martanin da suke mayarwa kan wani labari ko sharhi da ku ke wallafawa a CRI Hausa Facebook.

Shawara ta ita ce, ku rika zabar biyu ko daya daga cikin irin wadannan martani ko ra'ayoyin da masu sauraro ke rubutawa a shafinku na Facebook domin gabatarwa cikin shirin ku na Amsoshin Wasikunku na kowacce ranar Lahadi. Wannan yana da muhimmanci sosai wajen kara armashin shirin, duk da cewa akwai karancin lokaci tattare da wannan shiri amma ya dace ku yi nazarin wannan shawara tawa.

Na gode.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China