in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gaisuwa!
2016-08-15 13:47:29 cri
Ni hao,

Ina so zan mika sakon gaisuwa ta musamman zuwa gareku a sashen Hausa na CRI. Da kuma yi muku fatan alheri.

A gaskiya mun kwana biyu ba mu yi mu'amala ba a tsakaninmu, saboda haka a yau naga ya dace in aika muku da wannan gaisuwa. Kuma ina so ku sani cewar muna tare da ku a kullum.

Na samu labarin Malam Murtala ya kusa komawa kasar Sin bayan kammala aikin sa na 'yan shekaru a nan Najeriya. Ina so ku sani cewar, kamar yadda muka saba, zamu ci gaba da bayar da shawarwari nagartattu ga duk wanda zai zo nan Abuja domin karbar hannun malam Murtala don gudanar da aiki. Kuma ina yi wa wannan bako marhabin da zuwa a duk lokacin da zai zo.

A karshe, ina fata zaku ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

Ku huta lafiya.

Naku,

Salisu Muhammad Dawanau

Abuja, Najeriya

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v Fatan alheri tare da godiya 2016-08-15 13:43:13
v South China Sea 2016-07-11 14:50:22
v Shawara ga CRI Hausa 2016-06-26 11:12:12
v Bikin gargajiya na Duanwu ya bani sha'awa sosai 2016-06-14 17:23:34
v Watan Ramadan mai albarka 2016-06-06 14:32:53
v Ziyarar Murtala Zhang a birnin Daura ta kara mana ilimi 2016-06-06 14:31:10
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China