in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Murtala Zhang a birnin Daura ta kara mana ilimi
2016-06-06 14:31:10 cri

Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa na CRI suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake a nan Kano.

Ina farin cikin sanar da ku cewa, na samu damar sauraron sabon shirin ku na "Allah daya gari bamaban" na ranar Jumu'a 3 ga watan Yuni, wanda malamai Lubabatu Lei da Ibrahim Yaya suka gabatar mana dangane da ziyarar da malam Murtala Zhang ya kai a tsohon garin Daura dake jihar Katsina.

Abin da ya fi burge ni cikin shirin shi ne hirar da aka yi da masanin tarihi dake fadar sarkin Daura malam Ibrahim Hamisu wanda ya bayyana cewa birnin na Daura shi ne tushen Hausawa, duk da cewa birnin Kano ne ya fi sauran biranen kasar Hausa shahara.

Sai dai ra'ayi na ya zo daidai da na malam Ibrahin Hamisu wanda ya ce, labarin Bayajidda kakan Hausawa gaskiya ne, ba kamar yadda wasu ke zargin cewa labarin nasa tatsuniya ce kawai. Dalilin da ya sa na gaskata wannan lamari shi ne, har yanzu takobin Bayajidda tana nan a gidan sarki kuma ita ma rijiyar Kusugu na nan a birnin Daura mai son kallo kofa a bude take a koda yaushe.

A saboda haka, ya zama wajibi a duk inda al'ummar Hausawa suke to su rika girmama birnin Daura kasancewa shi ne, asalin Hausa 7 da banza 7 ('yan uwa 7).

Godiya mai yawa ga sashen Hausa na CRI bisa kawo mana wannan shiri mai ilimantarwa, sa'an nan godiya ta musamman ga malam Murtala Zhang bisa wannan tsaraba da ya kawo tun daga birnin Daura, jihar Katsina.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China