in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin gargajiya na Duanwu ya bani sha'awa sosai
2016-06-14 17:23:34 cri
Zuwa ga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin CRI CIBN.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ga baki dayan ma'aikatan ku a birnin Beijing, da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Hakika na ji dadin sauraron sabon shirin ku na "Allah daya gari bamban" na jiya Jumu'a 10 ga watan Yuni, inda malamai Lubabatu Lei da Maman Ada suka gabatar mana dangane shahararren bikin nan na gargajiya a kasar Sin wato Duanwu.

Kodayake, na dade ina kallon wannan biki na Duanwu ta hanyar mujallu da hotunan bidiyo amma ban taba sanin ainihin dalilin da ya sa al'ummar Sinawa ke gudanar da wannan biki ba. Na dade ina hasashen bikin Duanwu biki ne na gasar tseren kwale kwale kawai, amma yanzu bayan da na saurari wannan shiri naku na samu karin haske dangane da tushen wannan biki mai ban sha'awar gaske.

Labarin malam Qu Yuan wanda ake alakantawa da wannan biki na Duanwu na da ban tausayin gaske musamman yadda ya sadaukar da rayuwarsa domin ya nuna tsananin bakin cikinsa dangane da yadda daular Qi ta mamaye daularsu ta Chu a shekarar 278 kafin haihuwar Annabi Isa A.S. Wannan ya tabbatar da cewa akwai mutane masu kishin kasa tun a zamanin dauri.

Daga cikin al'adun bikin na Duanwu batun abinci mai suna Zongzi ya ja hankali na, domin na fahimci cewa kowanne bikin gargajiya na kasar Sin yana da irin nasa abincin, wato kamar yadda Jiaozi ya fi shahara a yayin bikin bazara ko Chun jie da Sinanci.

A ra'ayi na, bikin Duanwu yana daga cikin bukukuwan gargajiya na Sinawa dake jan hankalin mutane ba wai kawai Sinawa ba har ma da baki 'yan kasashen ketare, domin ya riga ya zama wata al'ada da ake dangantawa da Sinawa a duk fadin duniya. Ina fatan wata rana zan samu ikon kallon bikin Duanwu da ido na.

Mun gode muku kwarai da gaske bisa kawo mana wannan sabon shiri da ya nishadantar da mu.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v Watan Ramadan mai albarka 2016-06-06 14:32:53
v Ziyarar Murtala Zhang a birnin Daura ta kara mana ilimi 2016-06-06 14:31:10
v Sakon ta'aziyya 2016-06-06 14:29:19
v Watan azumin bana a kasar Sin 2016-06-06 14:27:55
v Ra'ayin ta'aziya 2016-06-06 14:25:59
v Akwai alfanu wajen yaki da matsalar kutsen yanar gizo 2016-06-02 08:53:47
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China