in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantaka tsakanin kasar Sin da Afirka ta kuma bude sabon shafi na nasara
2016-04-18 09:40:37 cri
Zuwa ga Malama Fatima Liu CRI Hausa,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan dukkanin ma'aikatan sashen Hausa suna Lafiya.

Bayan haka dalilin wannan rubuto muku sako na imel, shine a yau wato 15/04/16 ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya kawo karshen ziyararsa a kasar Sin a bisa gayyata da mai girma Shugaban kasar Sin Xi Jinping yai masa inafatan Shugaba Xi zai kawo irin wannan ziyara a kasar Najeriya nan gaba domin kuma bunkasa wannan ziyara. Rahotanni da kuka gabatar a shirye shiryanku na yau kan wannan ziyara sunyi kyau sosai gaskiya dangatar Najeriya da kasar Sin ta diflomasiyya na shekaru 45 an samu bankasuwa ta nasarori a fanni daban-daban, cudanyya tsakanin sin da najeriya tana samun cigaba ako yaushe, naji dadin hirar da Saminu Alasan Da malama Amina sukayi ta wayar tarho da shugaban kasa PMB kuma mu kanmu mun shaida cewa harkar layin dogo kamar daga Lagos zuwa Kano, Kaduna zuwa Abuja, da kuma harkar matatun mai tabbas kasar Sin suna bada gudunmawa gurin bunkasuwarsu, banda haka naji dadin yadda gwannoni suka kulla yarjejeniya taci gaba a kasar Sin, banda naji jin yadda shugaba PMB yai yarjejeniyar amfani da kudin kasar Sin.

A karshe inai muku fatan alheri.

Wassalam, Abdulkadir Ibrahim, G.C.L.C Kano.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China