in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sako daga malam Ishaq Abdullahi Dan Rimi Bena
2016-04-18 08:43:32 cri
Da fatan ziyarar da shugaba Buhari keyi a kasar Sin zata kara dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu domin kasar Sin kasa ce mai taimakawa kasashe masu tasowa a fadin duniya musamman ma yankin afrika, wannan ziyara da shugaban kasar Nijeriya Muhammad Buhari keyi wani babban ci gaba ne a wannan lokaci sabanin shekarun da suka shude, mu dai 'yan nijeriya kakarmu ta yanke saka a wannan mulki, domin tun hawan shugaba Muhammadu Buhari mulki mun samu ci gaba domin tafeye tafeyen da yayi ya kawo ci gaba. Hakika mun samu canjin gwamnati a kasar nijeriya , na saurari Radiyon Najeriya Kaduna cewa yau da safe cewa kasar Sin (China) zata ba da tallafin karin Ilimi ko karatu (Scholarship) 700 ga yan Nijeriya muna fata kasar Sin zata cika wannan alkawalin na tallafi domin yan nijeriya su amfani, Allah yayi muna jagora amin.

DAGA MAI SAURARONKU AKO YAUSHE

ISHAQ ABDULLAHI DAN RIMI BENA

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China