in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin Hausawa a kasar Sin kashi na uku: Garin masoyi ba ya nisa
2016-04-18 09:07:26 cri
Alhaji Sani Alhassan Tsoho, Bahushen Najeriya ne sananne a Guangzhou na kasar Sin musamman idan aka yi bayanin kasuwanci da kuma Hausawa da suka samu soyayya suka yi aure a kasar Sin. Wannan shirin yayi tsokaci ne baki daya ga yadda aka yi suka hadu da matarsa Halima, Basiniya, da kuma yadda suka yi soyayya har abin ya kai ga auratayya. Ma'auratan suna da 'ya'ya biyu, A'isha da Hauwa.

Shirin ya nuna mana labarin masoyan biyu, duk kuwa da irin kalubale da suka samu a baya kafin auren su amma dai an samu bunkasuwa sosai, babu matsala a bangaren bambancin al'ada da abinci ko zamantakewar aure. Sun samu fahimta sosai.

A takaice, ina iya cewa wannan shiri ya kayatar ainun, kuma akwai darussa na rayuwa wadda ya kamata ma'aurata su yi la'akari da kuma yin koyi da abin musamman wadanda ke da bambancin al'ada musamman ma ga wadanda ba 'yan kasa daya ba.

Shi ma wannan shiri zai yi kyau idan kuka kara fadada shi, kuka bincika labarin wasu 'yan Najeriya da suka yi aure a kasar Sin din domin soyayyar dake tsakaninsu saboda kara fahimtar da mu 'yan Najeriya da Nahiyar Afirka baki daya.

A ra'ayina, wannan shiri yazo daidai a lokacin da kowa zai so shi har kuma a samu fahimta na siyayya da auratayya. Kuma zai yi kyau idan kuka ci gaba shirya irin wannan shiri saboda amafanar da masu saurare da kallo wajen nishadi da karin ilimi.

Kun cancanci yabo sosai bisa ga wannan namijin kokari da fadakarwa.

Naku

Salisu Muhammad Dawanau

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China