in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Shugaba Xi Jinping ta kwana 3 a jahuriyar Czech
2016-03-30 16:12:23 cri
Zuwa ga Fatima Liu sashen Hausa na CRI Beijing, P.R. China,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan dukkanin ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya.

Bayan haka dalilin rubuto muku wannan takarda tawa shine, domin in nuna farin cikina game da ziyarar shugaba Xi Jinping ta kwana 3 a kasar Czech bacin shekaru 67 da kafa huldar jakadanci ina fatan shugaba Xi da takwaransa na Czech wato faraminista Bohuslav Sobotka zasu kuma bunkasa fannin tattalin arziki da zamantakewa a tsakaninsu. Inayi musu fatan alheri a wannan ziyara, sannan inasan jajantawa kasar pakistan abisa harin kunar bakin wake da yafaru a Lahore, banda haka ina kuma jajantawa wanda gobara ta afkawa Kano, Kebbi da sauran bangarorin Najeriya, sannan godiya ta musammmam ga Mr. Lee dan kasar Sin mai kamfani a Kano gurin aikowo da motocinsa na kashe gobara wanda sun taimaka sosai gurin kashe gobara. Inai muku fatan alheri. Nagode.

Wassalam, Abdulkadir Ibrahim, Great Wall CRI Listeners Club, Kano.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China