in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar bayi ta duniya da shirinku na kiwon lafiya
2016-03-28 09:20:56 cri

Zuwa ga sashen Hausa na CRI,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan kunanan lafiya. Bayan haka dalilin rubuto muku wannan imel shine gaskiya naji dadin rahoto da kuka gabatar akan ranar bayi ta duniya ranar da majalisar dinkin duniya ta kebe domin tunawa da yadda aka tursasawa mutane gurin shiga harkar bayi musammam bakaken fata na kasashen Afirka wacce daga shekarar 2007 duk ranar 25 ga kowane watan Maris na kowace shekara ake tunawa da wanda aka azabtar, gaskiya naji dadin babban Sakatare majaliasr dinkin duniya wato 'Bankimun' ina bibiyar labari da tarihin yadda aka bautar bayi da tursasu, na kalli shahararen fim dinnan wato 'The Roots' wanda akayi ashekarar 1977 wanda shahararen marubucin ya gabatar wato marigayi Alex Haley yayi kakansa na bakwai wato kunta kinte, na kuma kalli a kananan 12 years slave, gaskiya kebe wannan rana tana da mahimmamci. Banda haka naji dadin shirinku na kiwon lafiya wanda malama Tasallah take gabatarwa , lallai yara yakamata su dinga samun ishashshen bacci domin samun ingantacciyar lafiya, bayanai da aka gabatar sunyi kyau sosai ga ilimantarwa. A karshe inaso in mika sako na jaje ga 'yan kasuwar Sabon Gari a Kanon Dabo a bisa iftalayin gobara da lashe dumbin miliyoyin dubban Naira, ina musu jaje tare dafatan Allah ya maida alheri ya kuma kiyaye gaba, sannan 'yan kasuwar garin Kebbi suma ina musu jaji wanda wannan masifa duk a yau aka tashi da ita 26/06/2016.

Nagode, Wassalam, Abdulkadir Ibrahim, G.C.L.C Kano.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China