Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, na karanta wani sharhin labarai da malama Zainab Zhang ta fassara a a shafin ku na yanar gizo, jiya Laraba 3 ga watan Satumba, dangane da bikin farko da kasar Sin ta gudanar don tunawa da kawo karshen harin nuna karfin tuwo da Japanawa suka kaddamar a kan kasar Sin na tsawon shekaru 14.
Koda yake, yanzu shekaru 69 kenan da kawo karshen kisan kare dangi da kuma nuna tsantsar rashin imani ga al'ummar Sinawa da sojojin kasar Japan suka aiwatar a kan doron kasar Sin, amma abu ne mai wuya al'ummar duniya musamman Sinawa su manta da wannan lamari.
Hakika, zartar da dokar tunawa da wannan rana a duk ranekun 3 ga watan Satumba da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a ta yi ya dace, kai, ni a ganina ma an dan makara, ya dace a ce tun tuni an yi haka. Saboda bikin, zai zama wata alama da kuma jimamin rashin wadanda wannan ta'asa ta rutsa da su. Sa'an nan, zai ba da dama ga al'ummar wannan zamani su koyi darasi tare nuna bukatar martaba rayuka da kuma dukiyoyin al'aumma.
Fata na shi ne, duniya ta kasance wani dandali na zaman lafiya, walwala da jin dadi ga kowa, tare da yin hakurin zama da juna ciki lumana game da kokarin warware kowanne irin sabani ta hanyar tattaunawar sulhu ko shawarwari, maimakon zubar da jinin juna.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kano Dabo, Nigeria