A ranar juma'a 22 ga watan August shekara ta 2014 da yammaci, na saurari shirinku na 'Alla-daya Gari Bambam wanda malamai Danladi da Mamman Ada suka gabatar. Inda shirin ya maida hankali akan yadda gwamnatin jamhuriyar jama'ar Sin suke bada muhimmanci ga bada ilmi mai inganci ga yara kanana wanda hakan muhimmin batu ne kuma mai kyau ga makomar rayuwar yara manyan gobe. Babu shakka, wannan muhimmin kulawa da bada muhimmanci ga ilmin yara kanana a kasar Sin, babban abun yabawa kuma wata alama ce dake alamunta matsayin gwamnatin kasar Sin na bada kulawar masamman ga rayuwar yara dan inganta rayuwarsu anan gaba. Banda wannan, ina kira ga sauran kasashen duniya masamman ma kasashenmu na Afirka masu tasowa da su hanzarta yin koyi da shugabannin kasar Sin wajen samar da ingantatciyar rayuwa ga yara kanana tun daga tushe ko matakai da suka dace na wadata al'umma da ilmi, domun wadata al'ummar kasa da ilmi tun suna yara kanana ka iya haifar da kyakkyawar makoma ga yara da ma kasa baki daya.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.