Babu shakka, ziyarar kwanaki 5 da shugaban kasar Zimbabbwe mr. Robert Mugabe da tawagarsa suka fara a jiya asabar 23 ga watan august shekara ta 2014 a kasar Sin, muna iya cewa, kasashen 2 suna fadada kyakkyawar alakar diplomasiyya da cinikaiya da musayar al'adu da mutanta juna. Kana Kasar Sin da zimbabwe suna iya cimma burinsu na samun bunkasuwa tare bisa manyan tsare-tsare da hadin gwiwa a tsakaninsu. Kuma Sin, tana iya dukkan abunda za ta iya wajen taimaka wa kasar Zimbabwe ta fannin aikin gona da tattalin arziki da ilmin da dai sauransu. Ban da wannan, ina mai yaba wa gwamnatin jamhuriyar jama'ar Sin bisa kokarin da Sin take yi ga kasashenmu na Afirka masu tasowa. A shekarun 2005 da 2006 da 2010, mr. Mugabi ya kai ziyara a kasar Sin, mun yi imani cewa, Sin za ta ci gaba da cimma burikanta na samun bunkasuwa tare da aminanta na Afirka baki daya ba tare da kasala ko gajiyawa ba.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.