Babu shakka, akwai bukatar dake akwai ga sauran kasashe takwarorin kasar Sin, wajen yin koyi da kyakkyawar aniyar kasar Sin na bada tallafin magunguna da kuma tura kwararru masana kiwon lafiya ga kasashen yammacin Afirka dake kokuwa da yaduwar cutar Ibola mai kisan jama'a nan take ba tare da yin jinkiri ba. A ranakun 11 da 12 ga wata ne, kayayyakin magunguna tare da wasu kwararru n kiwon lafiya su 9 da kasar Sin ta tura su kasashen: Gunea, Liberia da Saliyo suka isa kasashen 3. Yawan kudin da gwamnatin kasar Sin suka kashe wajen gudanar da wannan muhimmin aikin jin kai da bada agajin gaggawa, ya kai kudin kasar Sin RMB milyal 30, al'amarin da ya nuna karara cewa, Sin tana nuna damuwarta ainun bisa halin takaici da zaman zullumi da al'ummomin kasashen 3 suke ciki a yammacin Afirka adangane da bullar cutar Ibola a kasashensu. To, yanzu dai, muna iya cewa, Sin ta cancanci babban yabo bisa namujin kokari da bujunta da suke yi wajen dakile yaduwar cutar Ibola a kasashenmu na yammacin Afirka, masamman ma kasashen Liberia, Gunea da Saliyo inda suka fi kowace kasa a yankin yawan mutanen da suka harbu da cutar Ibola.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.