Tabbas yau na saurari shirinku na kiwon lafiya, inda aka yi bayani a kan sinadarin Vitamin A. Wannan bayani ya kara mana fahimta a kan wannan sinadari, ko da yake mafi yawan al'ummar muna Afrika wadansu ba su san amfani da wannan sinadari ba domin kuwa wadansu suna hana a ba yaransu sinadarin vitanim A a lokacin da ake gudanar da allurorun cutar polio, a kan bayar da su ga yara a ko da yaushe, to amma rashin sani sai ka ga wadansu iyaye suna hana a ba yaransu. Ba shakka wannan bayani da cri hausa suka yi alhakika zai taimaka ga wadansu iyaye su bari a ba yayansu sinadarn vitim A.
Daga mai sauraronku a ko da yaushe Bello Abubakar Malam Gero, Sokoto, Nigeria.