in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakon jaje ga alummar Yunnan
2014-08-07 16:05:20 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa da fatan alheri ga ma'aikatan ku baki daya a birnin Beijing. Bayan haka, ina mai gabatar da sakon jaje na ga al'ummar Sinawa musamman wanda ke lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin bisa annobar girgizar kasa da ta aukawa garin. Lamarin da kawo asarar rayuka kimanin 589 a yayin da fiye da 1000 suka jirkata.

Ina jajantawa wadanda suka yi asarar 'yan uwansu da wadanda suka tsira da raunuka har ma da wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu. Da fatan ba za a sake samun aukuwar wannan bala'i ba, nake yi musu fatan alherin saurin farfadowa daga wannan tashin hankali tare da maye gurbin dimbin asarar da suka tafka sakamakon wannan girgizar kasa.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China