in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kasashen Afirka a birnin Washington Dc na kasar Amurka
2014-08-06 15:18:41 cri
A nawa ra'ayin, Amurka sun kira wannan taro na kasashen Afirka ne, da zummar dishashe tasiri da kwarjinin kasar Sin a nahiyarmu ta Afirka ne, ganin yadda kasashen Afirka ke ci gaba da cin moriyar Kasar Sin ta fannin tattalin arziki da musayar al'adu da diplomasiyya da samun bunkasuwa tare da Sin bisa manyan tsare-tsare da hadin gwiwa tsakanin sabuwar kasar Sin da kasashenmu na Afirka masu tasowa. Cikin kyakkyawar aniya ne, Sin take yin hulda da kasashenmu na Afirka dan kawo alheri da bunkasuwa ga jama'ar Afirka dake bukatar kasar Sin da kuma taimakon kasar Sin. Kuma kasar Sin bata san haddasa masifu da yake-yake a kasashenmu na Afirka da ma dukkan kasashen duniya baki daya. Tun bayan da kasashen Afirka suka kafa huldar diplomasiyya da cinikaiya da musayar al'adu tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka fiye da shekaru 50 da suka gabata ne, kasashen Afirka ke ci gaba da samun bunkasuwa a cikin lumana da fahimtar juna tsakaninsu da aminiyarsu sabuwar kasar Sin ta zamani. Dan haka, wannan yunkuri na kasar Amurka da kawayenta yammacin turai ba zai hana yaukakar huldar amunci dake samun ci gaba tsakanin Sin da Afirka ba, har abada.

Daga Malam Ali Buuge Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China