in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kabilar Hui musulmai sun burge ni sosai ainun bisa rarraba kayan abunci ga al'ummar gundumar Yunnan
2014-08-13 09:52:30 cri
Yaban gwani ya zama dole, aikin bujunta na bada agaji ga al'ummar Ludian dake lardin Yunnan na kasar Sin , bisa taimakon gaggawa na kayan abunci da musulmai yan kabilar Hui suka samar wa al'ummar yankin da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su a yankin Ludian dake lardin Yunnan na kasar Sin. Babu shakka, wannan abu ya burge ni kuma wannan babban abun yabawa ne ainun. Muna fata, sauran kabilun kasar Sin za su hanzarta yin koyi da yan kabilar Hui musulmai. Banda wannan kuma, muna kara yaba wa gwamnatin kasar Sin karkashin jagorancin shugaban kasar Sin malam Xi Jinping bisa aiwatar da aikin ceton al'ummar gundumar Ludian dake lardin Yunnan da masifar girgizar kasa ta abka musu, lamarin da ya sabbaba salwantar rayuka da dukiyoyin al'ummar yankin. A shekarun 2006 da 2008 da 2013 ma, sai da al'ummomin lardinan Sichuan da Gansu suka shaida abkuwar bala'in girgizar kasa, al'amarin da nan ma ya kawo muguwar asarar rayuka da ta dukiyoyin al'ummar lardinan 2.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China