A ranar asabar 02/08/2014 da sanyin safiya a wata masana'antar birnin kunshan dake lardin Jiangsu a sashin gabashin kasar Sin wani abu mai karar gaske ya fashe, lamarin da ya haddasa mutuwar Sinawa akalla 65 yayinda mutane 150 jikkata. Banda wannan, ina yaba wa jami'an asibitoci a lardin Jiangsu bisa kokarinsu na bada kulawar gaggawa ga mutanen da suka jikkata a masana'antar kana ina yaba wa masu bada agajin gaggawa a yankin adangane da aikin ceto cikin hanzari da suka yi a sa'ilin da lamarin ke faruwa a lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin. Bisa wannan lamari da ya abku a lardin Jiangsu, ina mika sakon ta'azziya da jaje ga gwamnatin kasar Sin da iyalai da yan uwan sinawan da wannan fashewa ta ritsa da su. Muna fata, hakan zai kara faruwa ba a kasar Sin anan gaba ba, amin.
Daga malam Ali Buuge Gashua.