Tare da fatan dukkanin ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ina mai farin ciki game da goyon bayan kasar Sin bisa yadda shugaba Xi jinping ya jaddada bin manufar nan ta ' Ka'idoji 5 na zama tare cikin lumana' a yayin bikin cika shekaru 60 da fara aiwatar da wannan manufa da aka gudanar ranar 28 ga wata.
Hakika, wadannan ka'idoji sun tanadi duk wasu matakai da zasu tabbatar da samun zaman lafiya, martaba iyakokin juna, da mutunta juna, game da rashin tsoma baki cikin harkokin gidan juna, tsakanin kasa da kasa. Bin wannan manufa sau da kafa ya taimaka wa kasar Sin wajen samun martaba tare da kyautatuwar dangantaka tsakaninta da makotanta har ma da sauran kasashen duniya. Domin tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da wannan manufa shekaru 60 da suka gabata kawo yanzu, Sin ta samu nasarar kaucewa shiga yaki ko wata zazzafar takaddama da makotanta ba, inda a bangare daya take kokarin kyautata dangantaka tare da nacewa wajen yin shawarwari ko bin sauran hanyoyin diplomasiyya wajen magance kowacce irin matsala domin kaucewa zubar da jini.
Dangane da haka, za a iya cewa kasar Sin ta bullo da manufar da ta dace da samun tabbatuwar zaman lafiya a duniya. Don haka, ya dace sauran kasashen duniya su yi koyi da kasar Sin wajen bin wadannan ka'idoji biyar na zama tare cikin lumana da juna, musamman a daidai wannan lokaci da ake ci gaba da samun sa-in-sa da a yawancin lokuta ya ke kaiwa ga gwabza kazamin fada tsakanin kasashen duniya sakamakon rashin martaba 'yancin juna ko tsoma bakin wata kasa cikin harkokin wata kasa.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria