Ko me ya sa, har zuwa yanzu kasashen Sin da Japan ba su kai ga cimma matsaya guda ba adangane da batun tsibirin Diaoyu wanda tun asalinsa mallakin kasar Sin ne kamar yadda tarishi ya nuna kuma dud duniya suka yi na'am da shi. Haka nan, ko me ya sa, sashin Hausa na cri kuka daina kawo mana rahotanni da labaru masu gamsarwa adangane da yanayin da ake ciki a mujadalar da kasashen Sin da Japan suke yi bisa jayaiyar ikon mallakar tsibirin Diaoyu na kasar Sin?. Kuma ga tsibirin Taiwan da Hongkong wanda suma kuka daina kawo mana rahotanni akansu. Mun gode muku kwarai da gaske.
Daga mai sauraronku a kullum, Alhaji Ali kiraji Gashua.