in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labarin birnin Handan tushen wasan Tai Chi ya ba ni sha'awa
2014-06-28 18:05:05 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri gare ku baki daya, ina fatan dukkan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ina farin cikin shaida muku cewa, na ji dadin sauraron shirin ku na 'Allah daya gari bamban' na yau Jumu'a 27 ga watan Yuni, wanda Malama Lubabatu da Maman Ada suka kawo mana bayanai dangane da ziyarar su a birnin Handan.

Hakika, labaran da malaman suka gabatar dangane da nau'in wasan Kung Fu mai suna Tai Chi ya burge ni kuma ya kayatar da ni, saboda wasan Tai Chi na da ban sha'awa sosai sakamakon yadda ake motsa jiki a hankali ba tare da wani gaggawa ba. Lamarin da ya sa tsofaffi a kasar Sin ke matukar sha'awar yin wannan wasa na Tai Chi, domin a yawancin lokuta ina ganin tsofaffi Sinawa ta akwatun talbijin suna yin wannan wasa na Tai Chi a wuraren shakatawa daban-daban dake birnin Beijing. Dalilin da yasa nake alakanta wannan wasa da tsofaffi kawai.

Amma bayan na saurari wannan shiri ilimi na dangane da wasan na Tai Chi ya karu, sakamakon jin cewa yau kimanin shekaru 23 kenan birnin Handan yana shirya gasar kasa da kasa ta wasan Taichiquan, lamarin dake nuna yadda wasan ya samu karbuwa ba wai tsakanin al'ummar Sinawa kawai ba har ma da na duniya baki daya. Lalle wannan wasa ya samu karbuwa a duniya yadda ya kamata.

Godiya ga al'ummar Sinawa da sauran hukumomin da abin ya shafa dangane da yadda suke tallafawa harkokin raya dadaddun al'adu irin wasan Tai Chi, lamarin dake bayar da dama ga sauran al'umma wajen kallo tare da kwaikwayon wadannan tsofaffin al'adu masu ban sha'awa.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China