in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka
2014-06-05 10:00:44 cri
Ni hao, da fatan kuna cikin koshin lafiya.

Jiya da yamma na karanta wani bayani a shafinku na yanar gizo mai nasaba da harkokin noma na zamani a kasar Mozambique wadda kamfanin kasar Sin Wambao ke bayar da taimako a kai bisa ga yarjejeniyar da suka kulla. Hakika, wannan labari ya bani sha'awa musamman ganin yadda yanzu wasu manoman Afirka ke amfana da dangantakar dake tsakanin Sin da mu.

Idan wasu kasashenmu na Afirka suka bi sawun kasar Mozambique bisa ga irin wannan tsari, na yi amanna wahalar abinci da ma wasu wahalolin zasu kaurace daga Nahiyarmu. Sanin kowa ne, Afirka ta samu kanta cikin wahalhalu amma dai muna fata alakarmu da Sin zata haifar da da mai idanu nan bada dadewa ba.

Fatan alheri mai yawa tsakaninmu da Sin a wannan karni, da ma nan gaba.

Naku,

Salisu Muhammad Dawanau

Abuja, Najeriya

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China