in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amsoshin tambayoyi
2014-06-05 09:12:03 cri
A gaskiya kasar Sin da jama'arta sun yi kokari ainun da nuna bujunta wajen samar da bunkasuwa da ci gaba ta bangarori masu yawan gaske a dogon lokaci da Sin da Afirka suka yi suna yin hulda da juna. Tabbas kasar Sin ta kawo bunkasuwar tattalin arziki da moriya mai yawa ga bunkasuwar kasashenmu na Afurka masu tasowa. Kuma na yi imani cewa, Sin tana da kyakkyawar manufa sosai ga kasashenmu na Afurka kuma cikin yakini ne kasar Sin take yin huldar diplomasiyya da cinikaiya da kasashenmu na Afurka masu tasowa. Babu shakka, gwamnatin jama'ar Sin da al'ummarta Sinawa sun yi kokari ga ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasashenmu na Afirka masu tasowa a cikin yakini, lamarin da ya sabbaba zaman cude ni in cude ka da cin moriyar juna a tsakanin bangarorin 2. A shekarar 1949 ne Sin ta aiwatar da shirinta na aiwatar da shirin yin kwaskwarima da kuma bude kofa ga kasashen waje inda kawo yanzu 2014, Sin da Afurka ke cin moriyar juna cikin daidaici da cin moriyar juna bisa manyan tsare-tsare da yin hadin guiwa a tsakanin Sin da Afurka. Dan haka, surutai da babatu da shirme da shatata karya tsagoranta inda suke cewa, kasar Sin ta je Afurka ne dan ta samu makamashi.To, hakika wannan batu ba haka bane, agaskiya ma dai Sin tana yin iya kokarinta wajen tsamo kasashenmu na Afurka daga kangin masifu da wahalhalu da kasashen mulkin mallaka na yammacin duniya suka tsundumamu a ciki. Ko tababa babu, kasar Sin ta kawo alheri mai yawa ga bunkasuwar kasashenmu na Afirka. Alal misali ma anan shine, kasar Sin ta gina babban zauren taro ga kungiyar hadin kan kasashen Afirka(African Union) kana Sin ta shafe fiye da shekaru 50 tana turo kwararrun likitoci zuwa kasashenmu na Afirka dan bada aikin jinya ga al'ummar kasashenmu na Afirka masu tasowa. Bugu da kari kuma anan shine, kamfanunuwan kasar Sin dake aiki a nahiyarmu ta Afurka suna aiyukan raya kasa masu inganci kuma kamfanunuwan kasar Sin suna daukan mutanen Afirka aiki dan su ma su ci moriyar aiyukan da sinawa ke aiwatarwa a nahiyarmu ta Afirka.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v Godiya ga CRI hausa 2014-05-30 16:22:41
v Matasa mata na kasar Sin suna nuna juriya 2014-05-27 20:43:49
v Ziyarar Faraministan kasar sin akasashenmu na afrika 2014-05-15 16:14:59
v Na saurari shirin 'Sin da Afirka' 2014-05-15 15:57:26
v Barka da ranar mahaifa mata! 2014-05-11 17:38:20
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China