in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a gaggauta daukan matakan dakushe hare-haren ta'addanci a kasar Sin
2014-06-05 09:15:29 cri
Zuwa ga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri, ina fatan baki dayan ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, na saurari shirin ku na 'Gani Ya Kori Ji' na ranar Laraba 28 ga watan Mayu, inda Malamai Ibrahim Yaya, Mamman Ada da Saminu Alhassan suka tattauna dangane da matsalar ayyukan ta'addanci a kasar Sin da ma duniya baki daya.

Na saurari bayanan gaba daya kuma tattaunawar ta yi dadi da ma'ana musamman bayanan da suka shafi sabbin matakan yaki da ta'addanci da hukumomi a kasar Sin suka dauka wajen tunkarar wannan bakuwar matsala da ta kunno kai a baya-bayan nan wacce al'ummar Sinawa kwata-kwata basu santa ba, sai dai su gani a jaridu ko kuma su saurara a sauran kafafen yada labarai.

Hakika, akwai abin ban takaicin gaske dangane da yadda matsalar ta'addanci ta bulla a kasar Sin, sakamakon yadda cikin dogon lokaci kasar ta Sin ta shahara a fannin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Lamarin da ya samar da wani kyakkyawan yanayin bunkasar tattalin arziki, zuba jari da kuma harkokin yawon shakatawa da bude ido. A ra'ayi na, zaman lafiyar da Sin ke da shi ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo saurin bunkasar tattalin arziki cikin shekaru 30 kawai da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, lamarin da ya burge duniya baki daya saboda ba a saba ganin saurin bunkasuwa irin haka ba.

Dangane da haka, bullar ta'addanci a kasar Sin wata babbar barazana ce ga makomar tattalin arziki da sauran manyan nasarorin da kasar Sin ta riga ta samu, domin matsalar ka iya haifar da cikas ga batun zuba jari daga ketare, kore masu yawon shakatawa, da kuma cusa tsoro ko zaman dar-dar a zukatan Sinawa da suka saba gudanar da rayuwarsu cikin walwala da 'yanci.

Lalle, ya dace hukumomi a Beijing su tashi tsaye kuma ka da su yi wani sassauci wajen fatattakar wannan annoba mai lalata kasa komai karfin arzikinta. Ina fatan kasar Sin, Nijeriya da ma duniya baki daya za su samu nasarar kawar da wannan matsala kacokan daga kan doron kasa.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon-Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v Amsoshin tambayoyi 2014-06-05 09:12:03
v Godiya ga CRI hausa 2014-05-30 16:22:41
v Matasa mata na kasar Sin suna nuna juriya 2014-05-27 20:43:49
v Ziyarar Faraministan kasar sin akasashenmu na afrika 2014-05-15 16:14:59
v Na saurari shirin 'Sin da Afirka' 2014-05-15 15:57:26
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China