Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ina mai farin cikain shaida muku cewa na ji dadin sauraron shirin ku na 'In ba ku ba gida' na yau Litinin 26 ga wata, wanda Malamai Kande Gao da Mamman Ada suka gabatar mana.
Ban da burge ni da wannan shiri ya yi na kuma koyi wasu darussa daga labarin matashiya Pang Jia wacce a halin yanzu ta samu babbar nasara wajen bunkasa sana'arta ta sayar da tufafi. Koda yake, wannan matashiya Pang Jia ta hadu da matsaloli na rashin samun goyon mahaifinta da kuma karancin ilimin kasuwanci tun da farko, lamarin da ya haifar mata da tarnaki cikin kasuwancinta, amma sakamakon nuna halin juriya da ci gaba da neman shawarwari ta samu kaiwa ga gaci a karshe. Har ma shi mahaifinta a karshe ya sauya ra'ayinsa wajen taimaka wa Pang Jia cikin harkokin kasuwancinta.
Saboda haka, akwai darussan rayuwa da za a iya koya daga wanann labari na Pang Jia, wato nuna juriya cikin mawuyacin hali ko yanayi na kawo cimma manufa, ban da wannan, labarin ya nuna cewa akwai bukatar yin bincike da neman sani dangane da kowanne kasuwanci kafin a fara. Abin da ya fi burge ni da labarin shi ne, Pang Jia daya ce daga cikin dubban mata matasa a kasar Sin da suka cimma nasarorin rayuwa bayan sun fuskanci kalubale iri-iri, wannan kuwa ya nuna halin juriya da matasan kasar Sin ke da shi.
Ina fatan mata matasa a kasata Nijeriya za su yi kwaikwayo da takwarorinsu na kasar Sin wajen nuna halin juriya da jarumtaka yayin da suke fuskanta kalubalen rayuwa.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria