in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na saurari shirin 'Sin da Afirka'
2014-05-15 15:57:26 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan dubun gaisuwa tare da fatan alheri, ina fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, na saurari shirin ku na yau Talata 13 ga wata, wanda malam Bako ya gabatar inda ya tattauna da wasu 'yan kasuwa biyu daga jihar Kano, wato malam Salisu Abdullahi da malam Ghali.

Hirar da malam Bako ya yi da wadannan 'yan kasuwa ta yi ma'ana sosai musamaman yadda suka bayyana irin tasirin da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ke kawo alheri mai yawa ta fannoni da dama wajen bunkasar tattalin arzikin nahiyar ta Afirka.

Kalaman wadannan 'yan kasuwa daga jihar Kano ya dada fitowa fili bayan da Firaministan kasar Sin Li Keiqiang ya kawo ziyara ga nahiyar Afirka ciki har da kasata Nijeriya a makon da ya gabata, inda Firaministan ya gabatar da wani jawabi mai karsashi kan taimakon kasar Sin ga nahiyar Afirka a wurin taron tattalin arzikin kasa da kasa

da aka gudanar a birnin Abuja.

Ni kaina na ji dadin sauraron jawabin na Li Keiqiang sakamakon inda ya yi bayani dalla-dalla dangane da manufofin gwamnatin kasar Sin na bayar da tallafi ga nahiyar Afirka, musamman inda Firaministan ya ce kasar Sin za ta ba da muhimmanci ga batun samar da ababen more rayuwa ga Afirka bisa la'akari irin koma bayan da nahiyar ke da shi ta wannan fanni. Wani abu da ya kara burge ni da jawabin Firaministan shi ne, batun tallafin kudi har dala biliyan 30 ga nahiyar ba tare da gindaya wasu sharudda ba. Wannan ya bayyana irin adalci da mutuntaka da ke tattare da manufofin kasar Sin ga nahiyar Afirka.

Fatan mu shi ne, dangantakar hadin gwiwa da ke tsakanin bangarorin biyu za ta ci gaba da bunkasa. Na gode.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Kanon-Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China