A ranar asabar 03 ga wata zuwa ranar lahadi 04 ga watan mayun shekara ta 2014 ne, aka dunga shatata ruwan sama mai hade da iska mai karfi a jihar Yobe, lamarin daya sabbaba malalar ruwan sama a tituna da gidajen jama'a. Banda wannan, ina mai yaba wa dukkan ma'aikatan sashin Hausa na Radiyo kasar Sin bisa kokarinku na samar wa masu sauraronku shirye-shirye masu dadin ji da kuma ilmi, masamman ma ganin yadda kuke yin kokari wajen fahimtar da mu masu sauraro a dangane da huldar diplomasiyya da cinikaiya da musayar al'adu da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare dake samun bunkasuwa a tsakanin Sin da kasashenmu na Afurka masu tasowa. Daga karshe, muna fata ziyarar da Mista Li Keqiang ke yi a kasashen Nigeria, Habasha, Kenya da Angola za ta kawo alheri da ci gaba da karin fahimtar juna da bunkasuwa a tsakanin Sin da Afurka, amin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.