Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, sabon shirinku na 'Allah daya gari bamban' da na saurara a yau Jumu'a 25 ya kayatar da ni, godiya mai yawa ga Malamai Lubabatu da Mamman.
Koda yake, malamai cikin shirin sun yi karin haske yadda ya kamata dangane da al'adar Sinawa ta son shan shayi musamman yadda suka dauki shayin a matsayin wani abinci na yau da kullum. Amma abin da ya fi burge ni shi ne, cewa al'adar shan shayi a kasar Sin ta fara ne a matsayin magani kafin daga bisani ta rikide zuwa al'adar Sinawa ta yau da kullum, musamman zamanin daular Tang shekaru 1,300 da suka gabata.
Hakika, duk mutumin da ke nazartar al'amuran da suka shafi kasar Sin zai shaida tasirin shan shayi cikin al'adun Sinawa, domin ko a fina-finan sinima na kasar Sin da mu ka dade muna kallo cikin akwatunan talbijin din mu an bayyana al'adar shan shayi ga iyalai, ko manyan jami'ai ko kuma karrama bako yayin da ya kawo ziyara. Ban da wannan, ga gidajen nuna wasannin Opera wanda suka shahara wajen samar da shayi ga masu kallo, game da gidajen shan shayi zalla masu tarin yawa a biranen kasar Sin.
Wannan ya sa na tuna da tawa ziyarar a kasar Sin cikin shekarar 2011, inda shayi ya kasance abinci na farko da aka fara karrama mu da shi yayin bikin bamu lambar yabo a dakin taro na gidan Rediyon kasar Sin. Hakika, wannan ya dada bayyana muhimmanci shayi cikin al'adar Sinawa.
Wani batun da ba zan taba mantawa da shi ba dangane da muhimmancin shayi a kasar Sin shi ne, yayin ziyarar mu a birnin Xi'an na lardin Shaanxi, ma'aikatan sashen Hausa da muka gudanar da ziyara tare wato Malama Fatima (Liu) da Malama Zainab (Zhang) sun siya mana wani shayi na kwalbar roba, wato na tafi-da-gidanka. Koda yake, wannan shayi ba bu sukari a ciki, amma dandanon sa na da dadin gaske.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria