Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan baki dayan ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ina farin cikin shaida muku cewa, na ji dadin sauraron sabon shirinku na 'Allah daya gari bamban' na jiya Jumu'a 11 ga watan Afrilu, inda Malamai Danladi (Jin) tare da Mamman Ada suka gabatar mana da bayanai masu dadin ji dangane da bikin Qingming na gargajiya a kasar Sin.
Kodayake, tushen wannan biki shi ne tunawa da kakannin-kakanni ta hanyar ziyartar kaburburansu tare da gudanar da aikin gyaran kaburburan, har ma da kawata kaburburan da furanni, kunna turaren wuta, ajiye kayan marmari, da sauransu. Amma a hakikanin gaskiya al'adar ajiye furanni a kaburbura yayin bikin Qingming ya fi bani sha'awa sosai, saboda furannin kasar Sin na da kyan gaske tare da ban sha'awa.
Wani abin ban sha'awa dangane da haka shi ne, al'adar Sinawa ta son furanni na da dogon tarihi, idan aka yi la'akari da irin dadaddun zane-zanen furanni na gargajiya dake da tarihin dubban shekaru wanda aka adana su a gidan nune-nunen kayan tarihi na fadar sarakuna dake birnin Beijing. Ciki kuwa har da zanen furanni da Sarki Hui Zhong na daular Song ya zana da kansa. Wannan ya sa na fahimci cewa, Sinawa suna matukar son furanni, bisa al'adar ta Sinawa kyautar furanni kyauta ce mai daraja.
Hakika, wannan ya sa na tuna da irin dimbin furanni masu ban sha'awa game da kyan launi da na gani yayin da a watan Satumba na shekarar 2011 muka samu halattar bikin nune-nunen fusahar kayan lambu na kasa da kasa wanda kasar Sin ta shirya a birnin Xi'an na lardin Shaanxi, bisa gayyatar Sashen Hausa na CRI. Ko shakka babu, a duk lokacin da na ji an ambaci kalmar furanni, to kasar Sin ce ke fara zuwa cikin rai na.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria