in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin yaki da gurbacewar muhalli a kasar Sin
2014-04-23 10:46:04 cri
A ranar talata 22 ga watan 04 shekara ta 2014, kasar Sin ta fara bikin yaki da gurbacewar muhalli tare gabatar da shawarwari daga masana akan muhalli da zai taimaka wa gwamnatin kasar Sin su dakile gurbacewar muhalli. Hakika bayanin da masana ilmin kare muhalli a kasar Sin irinsu, malam Han meng da malama Xia Muchen suka gabatar yayinda suke tsokaci da ba da shawarwari a gun bikin na bana, ya burge ni kuma ya kara min ilmi da karin fahimta a dangane da irin nau'in illolin da gurbacewar muhalli a kasar Sin ke haifarwa ga rayuwar jama'ar sinawa. Bayanin da masanan 2 suka yi a sa'ilin da suke jawabi a gun bikin, ya kara mun ilmin kare muhalli daga lalacewa kuma ni ma zai taimaka mun sosai tare da karin fahimta akan illar muhalli ga al'umma dama kasa baki daya. wannan biki akan kare muhalli dake wanzuwa a kasar Sin, babban abun koyi ne kuma wata alama ce dake alamunta matsayin kasar Sin wajen kasancewa kasa daya tilo a dud duniya wajen daukan matakan gaggawa tare da bada kariya mafi inganci ga yaki da gurbacewar muhalli a dud duniya.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban cri Hausa listeners club na jihar Yobe, Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China