in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nazarin kwararru akan ilmin likitanci da likitoci dake gudana a Florida ta kasar Amurka, ya kayatar da mu masu sauraro
2014-04-14 19:13:52 cri

A ranar litinin 14 ga watan April shekara ta 2014, na karanta wani saban nazari da kwararru a fannin ilmin likitanci da likitoci a jami'ar Florida ta kasar Amurka suke yi akan illar da cin abunci mai kunshe da maiko da kuma abunci mai yawan sukari ke haifar wa ga lafiyar maata masu dauke da juna 2. Lalle kam, wannan nazari da kwararru akan ilmin kiwon lafiya suke gudanarwa a jami'ar Florida ta Amurka, zai kara zaburar da milyoyin maata da iyalansu adangane da illar dake tattare da cin kayayyakin abunci mai kunshe da maiko da kuma sukari da ya wuce kima. Babu shakka a halin yanzu a ko ina a dud duniya, kayaiyakin abunci mai kunshe da maiko da sukari ya zama ruwan dare mai game duniya. Banda wannan kuma, nazarin ya bayanin karuwar yara masu yin kiba da matasa da suke ta'ammali da giya ko kuma yara matasa masu shan giya da magunguna da ya wuce kima suna kara karuwa sannu a hankali. Lalle kam, wannan ma babbar illa ne ga rayuwar yara kanana da matasa manyan gobe, kuma akwai bukatar dake akwai ga kwararru a fannin kiwon lafiya na kasar Amurka dama na sauran kasashe da su kara jan damarar gudanar wasu gwaje-gwaje da buncike sosai adangane da wannan matsala. Daga karshe, ina mai mika godiya ta masamman ga jagorar shirin kiwon lafiya wato, malama Tasallah wadda ta kawo mana wannam gudumowa.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China