Hakika jawabin da firaministan kasar Sin mr. LI ya yi a sa'ilin da yake bude taron dandalin Bo'oa na shekara ta 2014 wanda ake garin BO'OA dake lardin Hainan na kasar Sin, ya burgeni kuma ya nuna kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi wajen habbaka tattalin arzikin kasashen nahiyar Asia cikin hanzari. Babu shakka, kasar Sin cikin daidaici da lumana tana son a kafa wata kungiya da za ta taimaka sosai wajen ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasashen nahiyar Asia. Lalle kam, kasar Sin na da buri da manufofi masu armashi ga samar da moriya mai kyau da inganci da samar da yanayi mai kyau ga ci gaban kasashen nahiyar Asia. Dud da cewar, taron yana jan hankalin sauran kasashen duniya, muna da kyakkyawan fata da zato mai kyau ga cimma burin makasudun yin taron na wannan shekara da muke ciki ta 2014.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban CRI Hausa listeners club na jihar Yobe, Nigeria.