Salaam. A makon jiya, malama Tasallah ta yi tsokaci mai gamsarwa sosai adangane da illar dake tattare da cin abunci wanda ya wuce kima wato Mutum ya ci abunci mai yawa. Lalle kam, wannan tsokaci da malama Tasallah ta yi, ya kara mun fahimta da wayin kai adangane da kula da lafiya da yadda mutum yakamata ya dunga daukan matakan kaucewa daga kamuwa da cutar yin kiba wanda ke tattare da hadari ga lafiyar mutane.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, tarayyar Nijeriya.