in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
• Yau ne aka jefa kuri'ar zaben shugabancin Najeriya  2015-03-28
Tun daga safiyar yau ranar 28 ga watan Maris, aka fara zaben shugabancin tarayyar Najeriya a duk fadin kasar. Tuni aka yi shirin gama aikin tantance matsayin masu kada kuri'a da misalin karfe 1 na yamma, sai a fara jefa kuri'a da karfe 1 da rabi. Amma a wasu sassan kasar, aka samu matsala kadan wajen amfani da na'urar zamani mai tantance matsayin masu kada kuri'a, wato "Card Readers" a turance.
• Tasirin babban zaben Najeriya na bana ga makomar kasar 2015-02-12
Sakamakon matsalar tsaro da wasu sassan arewacin Najeriya ke fuskanta, ya sa hukumomin tsaron kasar suka baiwa hukumar zaben kasar mai zaman kanta (INEC) shawarar dage zabukan kasar da a baya aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2015 zuwa ranar 28 ga watan Maris, maimakon ranakun 14 zuwa 28 ga watan Fabrairu. Zabukan da masharhanta da dama ke kallo a matsayin matakin da zai zayyana alkiblar kasar nan da shekaru da yawa masu zuwa...
• Ana fatan za a gudanar da babban zabe a Tarayyar Najeriya yadda ya kamata, in ji masanan kasar Sin 2015-02-12
A 'yan kwanakin baya, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC ta sanar da dage babban zaben da ya kamata a yi a wannan Asabar din mai zuwa har sai nan da makwanni shida, sakamakon hare-haren da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ke yi a arewa maso gabashin kasar...
• Tasirin babban zaben Najeriya na bana ga makomar kasar 2015-02-11
Sanin kowa ne dai a baya hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta sanya ranar 14 ga watan Fabarairun dake tafe, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa, da na 'yan majalissar tarayyar kasar, ya yin da zabukan gwamnoni da na 'yan majalissun jihohi, zasu biyo baya a ranar 28 ga watan na Fabarairu...
• Dr. Mohamed M. Wada ya bayyana ra'ayinsa kan zabukan Najeriya 2015-02-10
Masharhanta da dama na ci gaba da bayyana albarkacin bakin su, game da dage babban zaben Najeriya, da hukumar gudanar da zaben kasar INEC ta yi...
• Hukumar INEC ta Najeriya ta shirya sosai don a gudanar da babban zaben shekarar 2015 yadda ya kamata 2015-02-09
• Masana sun yi kira ga Nijeriya da ta kafa cibiyar safarar kayayyaki ta yankin yammacin Afirka a birnin Lagos 2015-01-15
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China