in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan za a gudanar da babban zabe a Tarayyar Najeriya yadda ya kamata, in ji masanan kasar Sin
2015-02-12 16:00:14 cri

A 'yan kwanakin baya, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC ta sanar da dage babban zaben da ya kamata a yi a wannan Asabar din mai zuwa har sai nan da makwanni shida, sakamakon hare-haren da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ke yi a arewa maso gabashin kasar. Kudurin kuwa ya kara kawo rashin tabbaci ga yanayin zaben mai sarkakiya. Game da wannan sanarwa da ya abku ba zato ba tsammami, masanan kasar Sin a fannin harkokin kasashen Afirka sun bayyana fatansu na cewar kasar Najeriya za ta iya dora muhimmanci kan bukatun jama'a, da kuma yin musanyar ikon mulki cikin lumana.

Farfesa Attahiru Jega, shugaban hukumar INEC ya sanar a daren ranar Asabar din makon jiya 7 ga wata a Abuja, hedkwatar mulkin Tarayyar Najeriya, cewar sabo da sojojin kasar suna mai da hankali kan kungiyar masu tsattauran ra'ayi ta Boko Haram, ba za a iya ba da tabbaci ga tsaron zabukan ba, hakan ya sa aka jinkirtar da lokacin babban zabe zuwa ranar 28 ga wata mai zuwa na Maris, gwamnonin jihohi da 'yan majalisun dokokin kasar kuwa za a zabe su a ranar 11 ga watan Afrilu. Da zarar aka watsa wannan labari, nan da nan ya jawo hankulan kasashen duniya sosai. Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya sanar da cewa, yana fatan gwamnatin Najeriya za ta cika alkawarinta na shirya zabuka cikin lumana. Kungiyar ECOWAS kuwa ta ce, tana girmama wannan kudurin dage lokacin zabukan Najeriya. A waje daya kuma, wasu kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka sun nuna shakku kan wannan kudurin da gwamnatin Najeriya ta tsayar, inda Amurka ta nuna bacin ranta kan kudurin, har ma babban sakataren harkokin wajen kasar John Kerry ya yi wa gwamnatin Najeriya gargadin cewa, kada su kawo cikas ga yunkurin demukuradiyya bisa hujiyyar tsaron kasar.

Game da wannan, shugabar ofishin nazarin harkokin Afirka na cibiyar binciken kimiyyar zaman al'ummar kasar Sin Madam He Wenping tana ganin cewa, ko da yake wannan kuduri ya wuce abin da wasu mutane ke tsammani a zuciya, amma ya kamata a nuna fahimta a kansa. Ta kara da cewa, 

"Yanzu kungiyar ta'addanci ta Boko Haram tana ta kara kawo barazana ga zaman karko na al'ummar Najeriya, wanda ya kawo illa sosai ga zabukan kasar. Yanzu ana ta samun tashe-tashen hankali, har ma ba yadda za a yi sai gwamnatin kasar ta jibge 'yan sanda da sojojin tsaron lafiya don dakile kungiyar Boko Haram, idan an tsayawa shirya zabuka a wannan mumummin yanayi, to ba shakka ba za a iya tabbatar da lafiyar jama'a da tashohin kada kuri'a ba, har ma za a haddasa hargitsi mafi tsanani. Don haka a ganina, kudurin dage lokacin zabuka zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiyar al'umma da kuma zaman karko na siyasa, gami da babban zaben da za a shirya a karshen watan Maris."

Game da shakkun da wasu kasashen yammacin duniya suka nuna wa gwamnatin Najeriya, Liu Hongwu, mataimakin shugaban kungiyar nazarin harkokin Afirka ta kasar Sin bai amince da hakan ba. A ganinsa, ya kamata kasashen duniya su tallafa wa Najeriya wajen tabbatar da samun kwanciyar hankali a fannin siyasa, baya ga nuna goyon bayan gwamnatin kasar wajen gudanar da harkokinta yadda ya kamata. Yana mai cewa,

"Yanzu kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya suna sukar shugaba Goodluck Jonathan kan cewa, abin da ya yi ya kawo koma baya ga yunkurin samun demukuradiyya ta fuskar siyasa a Najeriya. Amma ina ganin cewa, dora matukar muhimmanci fiye da kima kan demukuradiyya da tsarin musayar ikon mulki a tsakanin jam'iyyu daban daban kawai, baya ga kauda kai ga bukatun kasashen Afirka na neman ci gaban tattalin arziki, da kuma wahalolin da Najeriya ke sha sakamakon hare-haren Boko Haram, lallai irin wannan suka ba za ta isa biyan bukatun Afirka ba."

Sakamakon mumumman yanayin tsaron da kasar Najeriya ke ciki da kuma tsarin jam'iyyun siyasa na kasar, mai yiwuwa ne babban zabe na wannan karo zai zama zabe mafi zafi tun bayan da jam'iyyar PDP ta rike karagar mulkin kasar a shekarar 1999. Duk da haka, a ganin masanan kasar Sin, sakamakon karuwar matsayin Najeriya a fannin tattalin arziki a wadannan shekarun da suka gabata, jama'arta su ba ta kwarin gwiwa. Yanzu yawancin 'yan Najeriya suna da aniyar kiyaye zaman karko a kasar, don haka ba za su yarda da ta da babban hargitsi a lokacin zabe ba, wanda zai lalata yunkurin ci gaban tattalin arzikin kasar.

Ban da wannan kuma, a bana, ban da Najeriya, akwai sauran kasashen Afirka da dama da za su gudanar da babban zabe, ciki har da Nijar, Togo, Sudan ta Kudu, Mali, Burundi da dai sauransu. Farfesa Liu Hongwu ya furta cewa, a matsayinta na wata muhimmiyar kasa a Nahiyar Afirka, gudanar da babban zabe cikin adalci da lumana a kasar Najeriya zai zama abin koyi ga sauran kasashen Afirka. Ya ce, 

"Bayan da kasashen Afirka suka bi tsarin siyasa na kasancewar jam'iyyu da dama har tsawon fiye da shekaru 20, lamarin abkuwar tashe-tashen hankali a ko wane zabe ya samu sauki a akasarinsu. Bugu da kari, yanzu kasashen Afirka da yawa suna samun bunkasuwar tattalin arziki. Duk wadannan sun samar da sharadi mai kyau ga aikin musayar ikon mulkin kasa. Don haka ina ganin cewa, ya kamata kasashen duniya su goyi baya da ba da kwarin gwiwa ga babban zaben Najeriya na wannan karo, ta yadda kasar za ta iya gudanar da shi yadda ya kamata. Najeriya kuwa ita ja-gora ce a Afirka, idan ya iya, to wannan zai ba da babban tasiri ga kwanciyar hankali a sauran kasashen Afirka."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China