in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tasirin babban zaben Najeriya na bana ga makomar kasar
2015-02-11 14:28:06 cri

Sanin kowa ne dai a baya hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta sanya ranar 14 ga watan Fabarairun dake tafe, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa, da na 'yan majalissar tarayyar kasar, ya yin da zabukan gwamnoni da na 'yan majalissun jihohi, zasu biyo baya a ranar 28 ga watan na Fabarairu.

Mako daya kafin gudanar zaben ne kuma hukumar ta INEC ta sanar da dage zaben da makwanni 6, matakin da ta ce ya biyo bayan shawarar da hukumomin tsaron kasar suka bayar, na a dage zaben domin a samu damar bada cikakken tsaro a dukkanin fadin kasar a lokutan zabukan.

Da dama dai daga masharhanta na kallon babban zaben na Najeriya dake tafe, a matsayin wani jigo da zai saita alkiblar kasar nan da shekaru da dama masu zuwa.

A wannan gaba da zaben Najeriyar ke karatowa, masharhanta da dama na kallon babban zaben Najeriyar a matsayin wata alkibla, da za ta fayyace makomar kasar a fannoni da dama. Ciki hadda muhimman batutuwan da a koda yaushe ke bakin 'yan kasar, da ma sauran masu fashin baki na ketare; kamar batun tsaro, da matsalar cin hanci da rasahawa, dake addabar kasar, da tabarbarewar ababen more rayuwa, da karancin ayyukan yi, da fatara, duk kuwa da kasancewar Najeriyar a sahun gaba a karfin tattalin arziki, da yawan al'umma a dukkanin nahiyar Afirka.

Jam'iyyun da ake fatan za su fi taka rawar gani a zaben na wannan karo su ne jam'iyyar PDP mai mulki, wadda shugaban kasar mai ci Dr. Goodluck Ebele Jonathan ke yiwa takara, sai kuma babbar jam'iyyar adawa ta APC wadda ta tsaida tsohon shugaban kasar ya yin mulkin soji, wato Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, wanda wannan ne karo na 4 da zai nemi wannan mukami a matsayin farar hula.

Wani abu da ya banbanta zaben na bana da sauran wadanda suka gabata, shi ne dunkulewar da mafiya yawan jam'iyyun adawar kasar suka yi waje guda, karkashin jam'iyyar kawance ta APC, lamarin da ya sanya masu fashin baki ke ganin a wannan karo, jam'iyyun biyu za su fafata matuka a zabukan na Fabarairu, sabanin ga misali zabukan shekarar 2011, inda baya ga PDP mai mulki, sauran jam'iyyu kamar ANPP da ACN da AFGA da CPC, suka samu wani kaso, a matakin zaben shugabancin kasar. Baya ga jam'iyyun Labour, da APGA da suka samu kujerun wakilci masu yawa, ciki hadda mukaman gwamnoni a wasu jahohin kasar.

Ko shakka babu batun tabarbarewar tsaro musamman a Arewa maso Gabashin Najeriya, na daga cikin manyan kalubale da hukumomin Najeriyar ke fuskanta a yanzu haka.

Ga duk masu bibiyar kafofin yada labaru dai sun kwana da sanin yadda mayakan kungiyar nan da aka fi sa ni da Boko Haram ke dada kaimi, wajen kaddamar da hare-hare a sassan Arewacin Najeriya, musamman ma jahohin Borno da Yobe da Adamawa, jahohin da gwamnatin tarayyar kasar ta kafawa dokar ta baci, a wani yunkuri na dakile yawaitar hare-haren dakarun kungiyar ta Boko Haram.

Ya zuwa yanzu dai hare-haren kungiyar sun janyo asarar rayukan dubban al'ummar kasar, tare da tilasawa al'ummun yankuna da dama kauracewa gidajen su.

Wani rahoton baya bayan nan da kungiyar kare hakkokin al'umma ta "Amnesty International" ta fitar, ya nuna cewa ya yin harin da dakarun kungiyar suka kaddamar a garin Baga a jihar Borno dake iyaka da kasar Chadi, a ranar 3 ga watan nan na Janairu, sun samu nasarar kwace wani sansanin sojin kasar, kana suka kaiwa al'ummar garin farmaki. Wannan hari ya kasance hari mafi muni da mayakan suka kaddamar a cewar rahoton, domin kuwa alkaluman kididdiga sun nuna cewa 'yan Boko Haram din sun kone garin baki daya, baya ga mutane kusan 2,000 da suka hallaka.

A cewar Amnesty cikin shekaru biyar da Najeriya ta yi tana fama da ayyukan wannan kungiya, dubban al'ummar kasar sun rasa rayukan su. Ciki hadda mutum kusan 10,000 da aka hallaka a bara kadai.

A daya hannun, tashe-tashen hankula masu alaka da ayyukan kungiyar sun tilasawa mutane sama da miliyan guda tserewa gidajen su, inda suke samun mafaka a wasu sassan na kasar. Ya yin da wasu duban 'yan kasar suka tsallaka iyaka zuwa makwaftan kasashe, kamar Chadi, da kamaru, da Nijar, domin tsira da rayukan su.

Lallai ko shakka babu, batun shawo kan matsalar tsaro a Najeriya zai kasance daya daga manyan kalubale da sabuwar gwamnatin dake tafe za ta fuskanta.

Game da batun tattalin arziki kuwa, duk da cewa Najeriya ce ke kan gaba a nahiyar Afirka, kuma kasa ta shida cikin jerin kasashe mafiya arzikin danyan mai, a wannan lokaci kasar na fuskantar gagarumin koma baya a fannin tattalin arziki, duba da yadda darajar danyan man ke ci gaba da karyewa a kasuwannin duniya. Wasu bayanai sun nuna cewa kasafin kudin kasar na shekarar 2015 wanda aka gabatarwa majalissar dokokin kasa a karshen shekarar da ta gabata, ba zai dore ba, idan aka yi la'akari da faduwar da danyan man ke kara yi. Ya yin da a hannu guda kuma, kasashe kamar Amurka da a da ke sayen man daga kasashen waje, a yanzu suka shiga sahun masu fidda man.

Farashin gangar danyan mai da a shekarar 2014 da ta gabata, ake sayarwa kan dalar Amurka 110, ta fara sauka tun daga watan Yunin shekarar bara, kuma sabanin hasashen da aka yi cewa farashin ba zai yi kasa da dalar Amurka 50, batun nan da ake yi farashin gangar man guda, ta yi kasa da dala 46 a ranar Laraba 21 ga watan Janairu.

Wani babban batu mai alaka da koma bayan da Najeriyar ke fuskanta a wannan fanni shi ne, dogaro da kasar ta yi kacokan kan cinikayyar danyan mai a matsayin hanyar samun kudaden shiga. Masharhanta da dama na gani ya zama wajibi sabuwar gwamnatin dake tafe, ta maida hankali matuka ga fadada hanyoyin samarwa kasar kudaden shiga, ta yadda kasar za ta rage dogaro kan albarkatun man fetur. Musamman ta hanyar bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu, da inganta harkokin noma, ta yadda al'ummar kasar za su samu karin guraben ayyukan yi.

Wata kididdiga ta nuna cewa kusan kaso 60 cikin dari na 'yan Najeriya na fama da matsalar rashin ayyukan yi, wanda hakan ke kara tsananta halin tsaro, da na zamantakewar al'ummar kasar.

Wani batu mai alaka da wannan shi ne batun magance cin hanci da rashawa, annobar da aka hakikance ta yi mummunan tasiri ga ci gaba Najeriya, har ma wasu na ganin ita ce jigon tabarbarewar ayyukan hukuma, da koma baya a fannin samar da ababen more rayuwa, kamar harkokin gudanarwa, da kiwon lafiya, da samar da isasshiyar wutar lantarki da ilimi da dai sauran su.

Bugu da kari sakamakon wannan zabe dai taka muhimmiyar rawa ga Najeriya, musamman a fannin kokarin hadin kan 'yan kasar.

Duba da cewa Najeriya kasa ce da ke da yankuna, da addinai, da kabilu daban-daban. Rarrabuwar kawuna da ake samu tsakanin 'yan kasar ta fuskar kabilanci, da kuma addini, sun taka muhimmiyar rawa wajen haddasa rikice-rikice a lokuta daban daban.

A baya an sha samun rikice-rikice da zub da jini tsakanin mabiya addinin musulunci da kirista, a sassan kasar daban daban, musamman a yankunan Arewaci da tsakiyar kasar.

Tasirin hakan ne ma ya haifar da batun karba-karba a mulki, ta yadda tun zaben shekarar 1999, shugaban kasa da mataimakin sa kan fito daga yankuna daban daban, kuma kusan dole ya kasance ba addinin su daya ba.

Wasu masharhanta na ganin hakan alamu ne, dake nuna tasirin rabuwar kawuna, da rashin amincewa juna tsakanin al'ummun kasar. Matakin da ke nuni da cewa ana iya zabar shugaba ne kawai, idan ya cika wasu sharudda masu nasaba da addini ko kabilanci, mai makon cancanta, wadda ita ce babban jigo a kasashen da suka ci gaba.

A yanzu haka dai INEC ta sanar da ranar 28 ga watan Maris a matsayin ranar gudanar zaben shugaban kasa da 'yan majalissun tarayya, ya yin da kuma zaben gwamnoni da 'yan majalissun jihohi zai biyo baya a ranar 11 ga watan Afirilu.

Ko shakka babu babban zaben Najeriya na wannan karo zai nunawa duniya alkiblar 'yan kasar game da ko sun gamsu da jagorancin jam'iyyar PDP da shugaba Jonathan ke wa takara, wadda ta kwashe kusan shekaru 16 ta na jagorancin kasar, ko kuma za su canza ta da jam'iyyar APC mai adawa, jam'iyyar da ta sha ikirarin cewa PDPn ce ta tsunduma Najeriyar cikin mawuyacin halin koma baya. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China