Wata sanarwar da shugaban gudanarwar kungiyar ta COMESA, Elizabeth Mutunga, ta bayyana cewa, ambassada Mohamed Ahmed Abdelghaffar Karrar shi ne zai jagoranci tawagar, jami'in wanda shi ne shugaban kwamitin dattawa na kungiyar COMESA wanda ya fito daga jamhuriyar Sudan.
Sanarwar ta ce shugaban tawagar wakilan zai isa kasar ne a ranar 17 ga watan Mayu, kwanaki hudu kafin gudanar da zaben.
A cewar sanarwar, masu sa ido na COMESA za su duba irin shirye shiryen da aka yi gabanin fara zaben wanda ya kunshi tuntubar jam'iyyun siyasar kasar, da hukumar zaben kasar ta Malawi (MEC), da jami'an tsaron kasar, da kungiyoyin fararen hula, da kafafen yada labarai, da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkokin zaben kasar. (Ahmad Fagam)