in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ba da tallafin jin kai ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Malawi
2019-04-05 15:55:11 cri

Kasar Sin ta ba da gudummawar sama da tan duba 6 na shinkafa da a kalla kudi dala dubu 300, a matsayin tallafin jin kai ga wadanda bala'in ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Malawi.

A jawabinsa yayin mika kayayyakin da ya gudana a Lilongwe, fadar mulkin kasar ta Malawi, jakadan kasar Sin dake Malawi Liu Hongyang, ya ce, al'ummar Sinawa na jajantawa Malawi kan wannan bala'i.

A nasa jawabin ministan tsaron cikin gida da daidaita bala'u na kasar Malawi, Nicholas Dausi, ya yaba da tunanin tausayawa na gwamnatin kasar Sin a wannan lokaci na kunci. Yana mai cewa, tallafin zai taimakawa wadanda bala'in ya raba da muhallansu matuka, da ma wadanda suka jikkata sakamakon bala'in na watan Maris.

Alkaluman sashen daidaita bala'u na kasar na nuna cewa, kimanin mutane dubu 869 ne bala'in ya shafa, yayin da wasu dubu 87 kuma suka rasa matsugunasu, kuma ke matukar bukatar taimako.

Gudummawar na zuwa ne, biyon bayan bala'in da ya yi sanadin mutuwar mutane 60 kana dubbai suka rasa muhallansu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China