in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron karawa juna sani kan hadin gwiwar Sin da Afirka da kuma ci gaban Afirka a Malawi
2017-09-08 10:36:57 cri
A jiya Alhamis ne aka bude taron karawa juna sani, game da hadin gwiwar Sin da Afirka da kuma ci gaban Afirka a birnin Lilongwe fadar mulkin kasar Malawi.

Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Malawi, da ma'aikatar kula da harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa ta Malawi ne suka shirya taron cikin hadin gwiwa.

A yayin taron, jakadan kasar Sin dake kasar Malawi Wang Shiyan ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu ci gaba a cikin shekaru kimanin 30 da suka gabata da take kokarin raya kanta, tana kuma son raba fasahohinta tare kuma da samar da taimakon kudade ga kasashen Afirka, bisa bukatunsu na neman ci gaba, da kuma habaka hadin gwiwar cinikayya a tsakanin Sin da Afirka yadda ya kamata.

Daga nasa bangaren, ministan harkokin wajen da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Malawi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, shekaru 10 ke nan tun bayan lokacin da aka kafa huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Malawi, kuma cikin wadannan shekaru, kasarsa ta sami wasu kyawawan damamaki karkashin bunkasuwar dangantakar dake tsakanin sassan biyu.

Haka kuma, ya ce, taron da aka yi, ya samar da kyakyyawar dama ga masana na kasashen Afirka, ta tattaunawa, tare da kuma yin koyi da juna, ta yadda za a amfana daga hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da kasashen Afirka yadda ya kamata.

A yayin taron, masanan da suka zo daga kasashen Sin, da Masar, da Tanzania, da Zimbabwe da dai sauran kasashe da jimillar su ta kai 11, sun tattauna kan batutuwa guda hudu, wadanda suka hada da, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a karni na 21, da kuma yadda hadin gwiwar Sin da Afirka zai tallafawa kasashen Afirka masu karancin bunkasuwar tattalin arziki da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China