in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotu a kasar Malawi ta bada belin ministan gona na kasar
2017-07-21 20:24:11 cri
Wata kotu a kasar Malawi, ta bada belin tsohon ministan gona na kasar George Chaponda, wanda jami'an rundunar 'yan sandan kasar suka cafke a ranar Laraba.

Hukumar ACB mai yaki da cin hanci da rashawa a kasar ce ta jagoranci damke George Chaponda, tare da wani mai suna Rashid Tayub, wanda ke jagorantar wani kamfanin hada hadar amfanin gona, bayan da ACBn ta zarge su da yin wata badakala, game da sayen masara daga kasar Zambia ba tare da kiyaye ka'idojin aiki ba.

Ana dai sa ran fara shari'ar Mr. Chaponda cikin wata mai zuwa, inda zai amsa tuhuma kan laifuka 3, da suka hada da saba ka'idojin aikin hukuma, da barnata dukiyar kasa, tare da mallakar kudaden kasashen waje ba bisa ka'ida ba, kamar dai yadda hukumar ta ACB ta bayyana.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China