in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malawi zata fara kwashe 'yan kasarta don kaucewa fadan nuna kyama a Afrika ta kudu
2019-04-04 10:30:31 cri
Gwamnatin kasar Malawi ta sanar cewa zata fara aikin kwashe 'yan kasarta wadanda fadan nuna kyamar baki na kasar Afrika ta kudu ya shafa.

Ma'aikatar harkokin kasashen waje da yin hulda da kasa da kasa ta Afrika ta kudun ne ta sanar da hakan a ranar Talata, tace kashin farko na 'yan kasar Malawin da fada ya rutsa da su ana sa ran za su iso kasar ne tun a ranar Laraba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rejoice Shumba ta fadawa kafafen yada labaran cikin gidan kasar cewa, ana sa ran adadin mutanen da za'a kashe a kashin farko za su kai mutane 35.

Ta ce akwai 'yan kasar ta Malawi kimanin 105 da suka nuna sha'awarsu ta komawa gida Malawi saboda suna tunanin rayuwarsu na fuskantar barazana a kasar ta Afrika ta kudu.

Shumba ta ce, wasu daga cikin 'yan kasar ta Malawi tuni sun bar sansanin da aka tsugunar da su kuma sun koma gidajensu yayin da wasu har yanzu suke zaune a sansanin kana suna fargabar cewa mai yiwuwa ne a sake kai musu hari duk da tabbacin da gwamnatin kasar Afrika ta kudun ta ba su cewa ta dauki matakan dakile hare haren.

A cewar gwamnatin Malawi, 'yan kasar ta Malawin 300 ne rikicin ya shafa kana biyu daga cikin har sun samu raunuka.

Gwamnatin kasar Afrika ta kudu da jam'iyyun hamayyar kasar sun yi Allah wadai da hare haren nuna kyamar baki a kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China