Za'a gudanar da laccocin ne a makarantu, hukumomin gwamnati, kamfanoni, wuraren taruwar al'umma, da kauyuka, inda kwararru za su dinga fadakar da al'ummar, da horar da jama'a game da yadda za su dauki matakan gaggawa da shiga aikin ceto, hukumar kula da bala'in girgizar kasa ta kasar Sin ce ta bayyana hakan a lokacin bikin kaddamar da laccoci a ranar Lahadi.
Bugu da kari, an bude shirin bitar tunkarar bala'in girgizar kasa da aikin bada agaji ta shafin intanet, inda aka bayyana kyawawan hanyoyin da za'a tuntakri annobar girgizar kasa.
A ranar Lahadi kasar Sin ta gudanar da bikin ranar yaki da bala'u min indallahi karo na 11, inda aka tuna da bala'in girgizar kasar da ya afku a Wenchuan a shekarar 2008, wanda yayi sanadiyyar mutuwa ko kuma bacewar mutane sama da 80,000.
An kaddamar da wannan ranar ne tun a shekarar 2009, da nufin wayar da kan al'umma game da matakan kariya daga afkuwar bala'u, da ilmantar da al'umma, da samar da horo game da yadda mutanen da suka tsira daga bala'u za su tafiyar da rayuwarsu.
Taken bikin na shekarar 2019 shi ne, yadda za'a karfafa aikin rigakafin bala'u da rage radadi, da kuma gina dabarun tsira da rayuwa, kamar yadda ma'aikatar kula da agajin gaggawa ta kasar Sin ta bayyana.(Ahmad Fagam)