in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ware Yuan miliyan 180 domin ayyukan jin kai a inda aka samu girgizar kasa
2017-08-11 10:06:54 cri
Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta ware Yuan miliyan 180, kwatankwacin dala miliyan 27.1, domin ayyukan jin kai, bayan wasu yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar sun fuskanci mummunan girgizar kasa 2.

Yankin Jiuzhaigou na lardin Sichuan da hukumar UNESCO ta ayyana a matsayin wajen shakatawa, kuma fitaccen wajen yawon bude ido, ya fuskanci girgizar kasa ranar Talata da ta gabata da misalin karfe 9 da minti 19 na dare agogon yankin, al'amarin ya yi sanadin mutuwar mutane 20 yayin da wasu 400 suka jikkata.

A Jinghe dake yankin Bortala na Mongolia a jihar Xinjiang kuwa, mutane 32 ne suka jikkata yayin da gidaje sama da 1,000 suka lalace sanadiyyar girgizar kasa da ta auku da safiyar ranar Laraba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China