in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu a girgizar kasar da ta aukuwa lardin Sichuan na kasar Sin ya kai 20
2017-08-10 20:35:01 cri

Hukumomi a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin sun tabbatar da cewa, yawan mutunen da suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 7.0 da ta aukuwa lardin a daren ranar Talata da dare ya karu zuwa 20, kana wasu 431 kuma suka jikkata

Rahotanni na cewa, an kwashe masu yawon shakatawa sama da 71,000, ciki har da 'yan kasashen waje 126 sakamakon wannan bala'i da ya aukuwa yankin Jiuzhaigou na lardin na Sichuan da misalin karfe 9 da minti 19 na daren ranar Talata, kuma zurfin girgizar kasar ya kai kilomita 20.

Jinzhaigou dai wani wurin yawon shakatawa mai tsauni da koramu ne da ya yi suna. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China